MAJALISSAR RUHU MAI TSARKI

Maraba da ziyartar wannan shafi, da fatan mun sadu a cikin cikakken lafiya. Manzo Daniel Yusuf Adamu daga majalissar Ruhu Mai Tsarki yake cewa Barka Da arzikin kasance wa tare da mu a wannan lokaci.

Mu na kyautata zaton cewa saduwan mu tana da alaka da wani kyakyawar shiri ta mussamman wanda Allah yake da shi domin mu. Ko dashiki ba lallai ne mu fahimci komai kai tsaye ba. Amma babu shakka shirin Ubangiji ne mu sadu a wannan lokaci.

Majalissar Ruhu Mai Tsarki dokaciya ce da yesu ya baiwa bawan sa, wanda ta kasance zumunta da ke hada kan matasa da ga dukannin dariku na ikilisiyar Almasihu daga arewacin Nijeriya, zuwa dukkanin aluma dake fahimta da kuma sadarwa cikin harshen hausa. Burin mu shine almajirantarwa irin ta littafi mai tsarki game da samun sabontuwar hankula, sakewar halaye da kuma dimanta domin zama kamar Yesu.

Fahimtar hakan ne ya bamu dama domin wallafa wannan shafi da bangaskiya cewa ruhu mai tsarki zai yi amfani da wannan sukuni domin ya ribato dukanan mai ziyartar shafin ga yesu almasihu, ya inganta bangaskiyar mu da kuma maishe mu santula masu daraja, kayan aikin sa domin girbi na mussamman.

Bari alherin yesu almasihu, da kaunar Allah Uba, da zumuntar Ruhu Mai Tsarki ya kasance da mu duka. Amin


SASHIN YIN RIJISTA (ONLINE MEMBERSHIP REGISTRATION FORM)